Gwamnatin Najeriya ta bayyana ranar Juma’a a matsayin hutun murnar zagayowar ranar demokradiyya ta shekarar nan.

Ministan kula da harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya bayyana haka a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa da ta samu sanya hannun babban sakataren ma’aikatarsa Georgina Ehuriah a Abuja.

Rauf Aregbesola
Ministan Kula da Harkokin Cikin Gida

Aregbesola ya kuma taya ‘yan Najeriya dake cikin gida da kasashen ketare murnar ci gaba da morar romon demokradiyya.
Sannan ya yabawa mutanen da suka jajirce wajen tabbatar ganin mulkin demokradiyya ya ci gaba a Najeriya.

Aregbesola ya kuma bukaci ‘yan kasa su ci gaba da ba gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari gudunmawar da ake bukata domin ci gaban Demokradiyya a Najeriya.

Ya kuma ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kokari na yaki da annobar korona da ta yiwa kasashen duniya katutu.
 

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *