Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aike wa Majalisar Dattawa sunan Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, domin amincewa da ita a matsayin Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari ya yi haka ne bisa damar da Kundin Tsarin Mulki ya ba shi.

Yanzu haka dai Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem ta na matsayin shugabar riko ce a kotun.

Monica Dongban-Mensem

Shugaba Buhari ne ya naɗa ta a muƙamin a cikin watan Maris, biyo bayan ritayar da Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa ta yi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *