AHMAD IDRIS
AKANTA JANAR NA NAJERIYA

Kwamitin dake kula da harkokin gudanarwar kudi na majalisar wakilai na barazanar bada umurnin kama babban Akantan kudi na Najeriya Ahmad Idris.

Shugaban Kwamitin Wole Oke, ya bayyana haka, ya ce sun yanke shawarar hakan ne saboda rashin amsagayyatarsu da Ahmad Idris ya yi.

Kwamitin dai na neman Akanta Idris ne domin ya kare zarge-zarge kan kashe kudade da aka kashe wajen yaki da annobar korona.

Oke ya ce idan Ahmad Idris bai bayyana a gaban kwamitin ranar 15 ga watan Yuni ba, za su yi amfani da karfin da kundin tsarin mulki ya basu na tilasta masa gurfana a gabansu.

A baya dai shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC, Chikwe Ihekweazu, ya bayyanawa kwamitin cewa hukumar ta karbi sama da naira billiyan 5.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *