A kalla Nera bilioyan 107.45 ne aka sakarwa wadanda aka yi wa tanadi, inda Babban Bankin Najeriya ta saki kudade domin yaki da cutar Korona a cikin kwanakin nan guda 90, kamar yadda bayanan da bankin ta fitar ya nuna.

Bayanan sun nuna cewa mutane da kamfanoni da ma’aikatu kusan su dubu shida ne suka karbi kudaden aro ya zuwa yanzu.

Daga cikin kudaden da CBN din ta fitar saboda annobar cutar Korona, akwa biliyan 100 na bangaren kiwon lafiya, da triliyon daya domin bai masana’antun noma da sarrafa kayayyaki, da kuma wata biliyan hamsin da aka tanadar domin baiwa iyalai da masu kananan sana’ao I aro.

Dangane da Nera Triliyan daya da aka sakar wa harkokin noma da kamfanin da ke sarrafa kaya, CBN ta basu biliyan tasa’in da uku da miliyan dari biyu domin bunkasa ayyukan su, a ciki akwai ayyukan 44 na Green Field da Brownfield.

Haka zalika bankin ya amince da sakin nera biliyan 10 da miliyan dari 9 ga wadanda suka nema su wajen dubu goma sha 4, a cikin biliyan 50 da aka tanada musu na bashi domin magidanta da kananan sana’o’i.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Wannan yayi kyau Allah ya karemu daga sharrin cututtuka na xamani ya yafemana laifukanmu Allah ya taimaki kasarmu najeriya da jahata Kano.