Ganin yadda jihohi a duk fadin Najeriya suke daukar matakai na budewa da saukaka wa jama’a dake fama da radadin rayuwa a jihohin su, har ya zuwa yanzu dai gwamnatin Jihar Kaduna na cigaba da rokon mutanen gari akan su jira kafin ta buga takardar da zata shata yadda za’a tsagaita rufe garin da dake dokar zauna a gida domin saukaka rayuwa ga jama’a.

A wata sanarwa da mataimakiyar gwamnan JIhar ta fitar, Hajiya Dr. Hadiza Balarabe, tayi alkawarin cewa za’a fitar da bayanan ne bayan babbar sanarwar gwamnati domin sanar da abubuwan da ake bukata.

A sanarwar, an tunatar cewa a makon da ya wuce, gwamnatin ta dage dakatar da dokar zauna a gida da wajen makonni biyu, kuma an bayyana cewa za’a yi magana da masu hannu da shuni kafin a yanke shawara.

To a yanzu dai gwamnatin tace zata tattauna da shugabannin gargajiya, da ‘yan kasuwa, da kasuwanni da kungiyoyin zirga-zirga da safara da shugabannin makarantu masu zaman kansu domin tattauina tsarin da za’a bi wajen komar da rayuwa akan turbar da za’a cigaba da harkoki cikin tsaro da walwala, a cewar mataimakiyar gwamnan.

A karshe dai mataimakiyar gwamnan ta bayyana cewa za’a fitar da bayanan yadda komai zai tafi kuma a amince da su sannan a buga kafin karshe wa’adin da aka kara shatawa na dokar zauna a gida, wato ranar Talata, 9 ga watan Yuni 2020.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *