MINISTAN LAFIYA NA NAJERIYA

Gwamnatin Najeriya ta ce mutane dari 9 da 79 ne suka mutu a kwanan nan sakamakon mace-mace da ba a saba gani ba a fadin jihar.

Ministan Lafiya Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan a wurin taron manema labarai na kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da korona ke shiryawa a Abuja.

Binciken da tawagar gwamnatin Najeriya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar ya nuna cewa mace-macen na da alaƙa da annobar cutar korona.

Ministan ya ce an samu rahotonnin mutuwar ne a ƙananan hukumomi takwas na cikin birni a watan Afrilun da ya gabata.

Ya ce an riƙa samun mutuwar mutane akalla 43 a kullum lokacin da cutar na kan ƙololuwarta kafin daga bisani adadin ya zama mutane 11 a kowacce rana.

Ya ƙara da cewa kusan kashi 56 cikin 100 na mace-macen sun faru ne a gida, yayin da kashi 38 suka faru a asibiti.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *