Jami’an sojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta kashe barayin shanu 70 a dajin Kachia da ke jihar Kaduna bayan wani aiki da ta kaddamar a yankin.

Mai magana da yawun rundunar Manjo Janar John Eneche, ya ce, runduna ta mussamman da ake yiwa lakabi da Operation Thunderstrike ce ta kaddamar da harin tare da hadin gwiwar mayakan sa-kai.

Wasu sassan arewacin Najeriya dai sun dade suna fama da hare-haren ‘yan bindiga masu satar shanu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *