Gwamnatin jihar Kano ta rabawa al’ummomin Fulani gidaje domin inganta rayuwarsu da harkokin kiwo a fadin jihar.

Gwamnan Kano, tare da mukarrabansa

Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci rabon gidaje kyauta a dajin Dansoshiya dake karamar hukumar Kiru karkashin kwamitin tabbatar samar da RUGA da kasuwar Nono karkashin da Jibrilla Muhammad ke jagoranta.

Ganduje ya ce kasancewar sa Bafulatani Makiyayi, ya zama wajibi ya tallafawa makiyayan wanda hakan zai inganta rayuwar su da ta yayansu.

Gwamna Ganduje

Gidajen dai 25 da aka kammala daga cikin gidaje 200 wanda Gwamnatin jihar ta sha alwashin ginawa a dajin.

Gwamnatin jihar ta ce za ta samar da rijiyoyin butsatse don shan ruwan shani a gurare 5 cikin dajin tare da aikin gina dam.

Haka kuma gwamnan jihar ya ce za a gina makaranta da asibitocin mutane da na dabbobi domin magance rigingimun makiyaya da manoma.

Ra’ayoyi 3

Your email address will not be published. Required fields are marked *