FYADE A NAJERIYA: BA DOKAR BA, ZARTARWA!

Shin da ‘yan Najeriya ke ta sa toka sa katsi a kan hukuncin fyade a kasar, dama ba dokar da ta ke hukunta masu aikata laifin fyade ne ko kuwa dai su ‘yan Najeriya ne ba su san da dokokin ba saboda karancin aiwatar da su?
Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

‘Yan Najeriya sun dau zafi a ‘yan kwanakin nan game da yadda maganar fyade ke neman fin karfin jama’a, inda a ke ta samun yawaitarsa ciki har ma da masu yin fyade tare da kashe wadanda suka yi wa aika-aikar. Abubuwan da suka faru kwanan nan a Kudanci da Arewacin Najeriya.

Inda a ka yi wa wata matashiya Uwavera Omozuwa ‘yar shekaru 22 fyade tare da kashe ta, a lokacin da ta ke kebe a wata cocin kusa da gidansu tana karatu a birnin Benin. Sai kuma wata yarinya ‘yar shekara 12 da wasu jerin maza guda 11 suka dade suna jima’i da ita a jihar Jigawa.

Hakika fyade yana cikin manyan laifuffuka a Najeriya, sannan idan a ka kama tare da tabbatar da shi ya kan kai wanda ya aikata ga samun daurin rai da rai.

Akwai dokoki a Najeriya da ke aiki a bangarorin Najeriya daban-daban tsakanin kudanci da arewacin kasar. Muna da kundin shari’a kamar kashi uku da zan lissafo daga kasa da kuma garuruwan da dokokinsu su ka shafa.

Na farko akwai kundin hukunta manyan laifuffuka da a ke kira da ‘The Criminal Code’ a Turance. Wannan kundin shari’a da shi a ke amfani a jihohin kudancin Najeriya.

Na biyu kuma shine, kundin shari’ar da a ke amfani da shi wajen hukunta laifuffuka a arewacin Najeriya da a Turance a ke kira da ‘Penal Code’.

Na uku kuma akwai kundin shari’ar da jihar Lagas kadai ke amfani da shi wajen hukunta manyan laifuffuka, wanda a kira a da ‘The Criminal Laws of Lagos’ a Turance.

Sai na hudunsu, wato kundin shari’ar na gwamnatin tarayya da wasu jihohi irin su Lagos da Anambra da Ebonyi da Oyo suka ara su ka yafa wajen hukunta laifuffuka masu nasaba da cin zarafi bil’adama mai suna ‘The Violence Against Persons Prohibition Act’ a turance.

Kundin shari’ar da jihohin kudancin Najeriya ke amfani da shi ya bayyana abubuwa ko aikin da idan mutum ya yi to ba shakka ya aikata fyade, idan a ka yi la’akari da Sashi na 357 da kuma na 358 na wannan kundi kamar haka;

“fyade shine aikata saduwar jima’in da ba ta bisa doron doka ga mace ko yarinya ba tare da amincewarsu ba, ko kuma sun amince ne ta hanyar tursasawa bayan an yi musu wata barazanar cutar da su ko kuma fargabar kar a illata su idan sun ki amincewa. Ko kuma yin badda kama a matsayin miji ga mace mai aure. Idan dayan wadannan abubuwa suka faru to zai iya jawo wa mutum har hukuncin daurin rai da rai a gidan wakafi.”

Shi kuma kundin hukunta laifuffukan jihohin arewacin Najeriya a karkashin Sashei na 282 sai ya ce, ana daukar mutum a matsayin wanda ya aikata fyade ne idan a ka same shi da aika-aika kamar haka:

“Duk namijin da ya sadu da wata babbar mace ko yarinya ta hanyar jima’i ta daya daga cikin wadannan hanyoyin da suka hada da, saduwa ba da muradin kanta bak o kuma amincewar ta ba, ko kuma da yardarta amma bayan an tsoratar da ita da cewa za a kasheta ko illata lafiyar jikinta.”

Shi kuwa Sashi na 258 na kundin hukunta manyan laifuffuka a jihar Legas cewa yayi;

“Duk namijin da ya aikata saduwar jima’in da bas hi da hurumin hallaci da babbar mace ko yarinya ba da yardar ta ba, to ya aikata fyade.”

A cikin Sashi na 1 a karkashin kundin da jihohin Lagos da Anambra da Ebonyi da kuma Oyo ke amfani da shi da suka ara su ka yafa daga gwamnatin tarayyar Najeriya cewa yayi;

“Mutum ya ko ta aikata fyade matukar a kay i kutsawar saduwar jima’i da gangan ta hanyar shiga gaban al’aura ko dubura ko kuma bakin wani ko wata da ma duk wani sassan jiki ba tare da izinin mutum ba ko kuma a ka sami amincewar amma ta karfi da yaji.”

Sai dai shi kundin hukunta laifuffukan tarayya da wasu kebabbun jihohin da muka ambata a baya cewa suna amfani da shi, ya dan kara buda bayani idan a ka lura ta hanyar hada lissafin aikata fyade ba maganar mace ko namiji, a idon wannan kundi duk lissafin laifin na bai daya ne ga mata da maza.

Sannan kuma a wani Sashin na sa ma ya kara da maganar aikata fyade daga mutum daya zuwa yin gangami a aikata fyade da mutum daya da a turance a ke cewa ‘gang rape’. Wanda wannan ne na farko a Najeriya da hukuncin ya bi ta kan masu gangamin aikata fyade a Najeriya.

Duk da wadannan dokoki da kuma tanadin hukuncin da ka iya kama wa daga cin tara har zuwa daurin da ka iya zama na rai da rai bisa yanayin yadda fyaden ya faru, to amma abu ne mai wahala ka ga an hukunta masu aikata fyade a Najeriya. Wanda bisa majiyoyi da dama sun nuna ‘yan tsirarin mutane ne a ka taba ganin hukuncin laifin fyade ya ritsa da su.

Musamman yadda abin ya ke da sarkakiyar tabbatar da aikata laifin na fyade ga wani ko wata. Domin kuwa akwai abubuwan da ke dagula lissafin tabbatar da faruwar lamarin.

Akwai maganar al’adun mutane na kokarin boye lamarin da sunan kar a tona wa juna asiri musamman ma idan abin ya shafi ‘yan uwan jini ko abokan arziki na kusa, da dai makamanta irin wadannan raunanan hujjojin.

Dabi’ar jin kunya da rufa-rufa na kara jefa wadanda a ke wa fyade a cikin garari da bakin cikin rayuwa. Al’umma na da bukatar canza wannan dabi’ar matukar ana son a ceci ‘ya’yanmu da jikokinmu daga sharrin fyade.

Amma fa wani hanzari ba gudu ba, a tabbatar ana tattara kwararan hujjoji duk lokacin da fyade ya auku ga wani ko wata don samun madafa a kotun shari’a don ita shari’a da hujjoji ta ke aiki ba da yanayin bacin ran mutanen da ke shari’a da juna ba.

Haka zalika sai an lura matuka da masu kage ko sharri ga wadanda kila kawai neman bata suna ne ya sa suka laka wa wani ko wata kazafin aikata fyade don wata manufa ta su.

Sannan dole mu koyar da ‘ya’yanmu da ‘yan uwanmu mata da maza sanin darajar mutumta juna musamman ta bangaren tsiraikcin juna. Mu kuma nuna musu dabarun yadda a ke gane mai niyyar aikata fyade mace ko namiji.

Daga karshe kuma gwamnatoci da kotuna su zage damtse wajen ganin ana amfani da dokokin da kundin shari’u na bangarorin Najeriya suka tanada don hukunta masu aikata fyade maza da mata kuma bai daya.

A dunkule kenan idan muka ce ‘Fyade a Najeriya’, sai mu cewa ‘Ba Dokar Ba, Hukuncin!’.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *