Gabannin mika yaki da COVID-19 zuwa jihohi kamar yadda gwamnatin tarayya ta bakin kwamitin shugaban kasa na yaki da COVID 19, akwai fargaba dake tasowa da kuma shakka akan shiryawar gwamanton jihohi wajen takalar annobar.

A Kaduna, gwamnatin ta samar da dakunan gwaji guda biyu da kuma wata mota wadda za’a iya yin gwajin da ita, kuma ana kyautata zaton zata iya yakar cutar amma wasu mazauna na fargabar cewa jihar baza ta iya cigaba da yakin ba ba tare da taimakon gwamnatin tarayya ba.

Jihar Kebbi kuma bata ma da wajen gwajin Korona, kuma ta dogara ne akan Sokoto. Sai dai gwamnatin jihar ta bayyana cewa likitoci da jami’an asibiti sun samu isashen horo domin takalar annobar. \

Gwamnatin Jihar Bauchi kuma ta samu amincewar hukumar NCDC domin yin amfani da dakin kimiyyar ta domin gudanar da gwajin Koronar, amma mazauna garin basu da kwarin gwiwar cewa hakan zai yiwu. Jama’a sun bayyana cewa babu kayan aiki, kuma gwamnatin jihar bata da niyyar gudanar da aikin yadda ya dace.

A Sokoto kuwa, dakin gwajin Korona ta kammala gwaji a kalla 698 kuma wasu mazauna sun bayyana karfin gwiwar su cewa gwamnatin jihar zata iya yaki da cutar yadda ya kamata.

Idan muka leka Gombe, gwamnati ta bayyana cewa a shirye take ta karbi akalar yaki da cutar Korona daga hannun gwamantin Tarayya.

Jihar Nassarawa bata da dakin gwajin Korona, amma tana da wuraren da aka shirya sun a musamman domin karbar yawun da ake gwadawa, kuma mazauna na rokon gwamnatin tarayya akan ta cigaba da karbar yawun har zuwa lokacin da annobar ta lafa.

Jama’ar Jihar Yobe sun bayyana shakka akan shirin gwamnatin ta wajen daukar nauyin yaki da korona ita kadai. Malamai sun yi korafin cewa babu cibiyar gwajin Korona, sannan ma’aikatan kiwon lafiya sun ce jihar ba a shirye take ba domin karbar akalar wannan yaki.

A Adamawa kuwa, mutane sun yi kafar ungulu da matakin bar wa gwamnatin jihar yaki da Korona, suna masu cewa babu isassun ma’aikatan kiwon lafiya da kayan aiki, amma kwamishinan kiwon lafiya na jihar Farfesa Abdullahi Isa ya bayyana cewa jihar na samu nasar wajen yaki da cutar ba tare da taimakon gwamnatin tarayya ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *