Labaran fyade na kara yawaita biyo bayan kisan da aka yiwa Vera Omozuwa a garin Benin. Vera dalibar microbiology ce a Jami’ar Benin, kuma Larabar makon da ya wuce ne wasu mutane da ba’a san ko su nawa bane, suka yi mata fyade a Majami’ar Redeemed Christian Church of God dake garin Benin, a lokacin da take karatu.

Rahotanni sun nuna cewa maza hudu ne suka daure hannun ta, suka rufe idanun ta sannan suka toshe bakin ta, sannan jini yayi ta zuba daga kanta wanda ya fashe bayan fyaden.

A garin Ibadan kuma babban birnin jihar Oyo, ‘yan uwa sun yi ta kuka a gidan iyayen Barakat Bello, dalibar Kimiyyar Noma mai shekaru 18 wadda rahotanni ke nuna cewa an kashe ta ne bayan an yi yunkurin yi mata fyade, amma ta ki yarda.  

A jihar Benuwe kuma, ana ta shari’a da wani tsohon malamin jami’a Andrew Ogbuja wanda ake zargi shi da danshi da yin fyade da kuma kashe wata yarinya Elizabeth Ochanya Ogbanje mai shekaru 13.

A jihar Cross River, an tsare wani tsohon Kyaftin din Soja Bassey Ekanem da zargin yiwa ‘yar dan uwanshi mai shekaru hudu fyade. Wani yaro mai shekaru biyu ya fallasa abun, inda ya ga mutumin yana saka hannun shi a cikin jikin yarinyar.

A jihar Kaduna, ana zargin wasu mutane hudu da yiwa wata yarinya mai shekaru 13 fyade bayan bata kwaya domin ta fita daga hankalin ta, daga baya kuma suka jefar da ita a karkashin wata kusa da gidan su. Yanzu haka dai, gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta tsare wadannan mutane kuma ana cigaba da bincike.

Har yanzu a Kadunan, an yanke wa wani mutum Usman Shehu Bahir hukuncin kisa ta hanyar rataya biyo bayan fyade da yayi wa wata yarinya mai shekaru 2 har hakan ya kai ga ajalinta a shekara ta 2015. An ce ya kai Fatima dakin shi ne, inda ya share mintuna 40 yana yi mata fyade har ta mutu.

A jihar Katsina kuma, ana zargin wasu maza masu aure su 9 da yiwa wata yarinya mai shekaru 10 fyade a kauyen Maigora dake karamar hukumar Faskari. Yanzu haka jami’an tsaro na cigaba da binciken lamarin.

A jihar Osun, wani mutum Moses Oloko mai shekaru 57 na fuskantar tuhuma na yin amfani da Nera 100 domin jawo hankalin wata yarinya mai shekaru 12 har sau 10 yana yi mata fyade. A halin yanzu yana kurkuku.

A Ekiti kuma wani yaro mai shekaru 15 ya tayar wa mutane hankali a lokacin da aka tuhume shi da yiwa wata yarinya mai shekaru 3 fyade a yankin Ido-Ekiti a cikin wannan makon.

A Ogun kuma jami’an tsaro sun tabbatar da tsare Wasiu Banko mai shekaru 25 inda ake zargin shi da yiwa wata mata mai shekaru 70, amma yace yayi hakan ne saboda ya sa giya.

A jihar Neja ma haka wani mai shekaru 25 na fuskantar zargin yiwa wata mata mai shekaru 85, inda yayi barazanar sace ta.

To ko meyasa fyade ke karuwa, masu fashin baki sun nuna cewa saboda yawan amfani da kafofin sada zumunta ne yasa ake gani kamar lamarin na karuwa, kuma yana baiwa wadanda aka yiwa fyaden karfin gwiwar fitowa su bayyana abunda ya same su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *