Alhamis dinnan ne aka bada rahoton wannan hari akan reshen First Bank dake garin Isanlu a karamar hukumar Yagba ta Gabas dake jihar Kogi, inda har yanzu ba’a tabbatar da adadin wadanda aka kashe ba.

An kuma bada labarin cewa maharani sun farmaki akan shedkwatar ‘yan sandar wannan garin, inda suka kashe mutane da ‘yan sanda wadanda ba a san yawan sub a.

Har yanzu ba a gama samun tabbatattun bayanai ba akan hare-haren.

Jami’in Hulda da Jama’a na yankin, DSP William Ayah ya bayyana cewa biyo bayan rashin samun nasara wajen yin magana da DPO da ma wasu jami’an, an baiwa mataimakin Kwamishinan ‘yansandar jihar alhakin tabbatar da abunda ya faru a wajen.

Masu gani da ido sun ce ‘yan bindigan sun je ofishin ‘yan sandan, inda suka kashe duk wani jami’i da suka gani.

Sun kuma kara da cewa maharan sun lalata abubuwa, sannan sun kwashi makamai.

‘Yan bindigan dai an ce sun kai bakwai sun tsaka a bankin First Bank a motoci biyu, inda suka kashe jami’an tsaron wajen, sannan suka shiga cikin bankin inda suka kashe ma’aikata da kwastomomi.

An kuma kara da cewa maharani sun share sama da mako daya suna cin karen su babu babbaka, kafin tafiya a cikin motocin su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *