An tsare wani mutum dan jihar Pennsylvania dake Amurka bayan kwarara wa wani yaro mai shekaru 4 man fetur da barazanar cinna masa wuta domin kona alhanin dake jikin shi, a cewar ‘yan sanda.

Josiah James McIntosh mai shekaru 27 na fuskantar laifin yunkurin yin illa da barazana ga rayuwar bil adama, da ma wasu laifukan. Wannan lamari ya faru ne misalin karfe daya Larabannan a wani gida dake karamar hukumar Southmont.

Jami’an tsaro sun isa gidan ne biyo bayan karar da aka kai musu na hatsaniya, inda suka samu McIntosh da yaron duk suna warin man fetur, sannan shi mai kare kanshi yana dauke abun kunna wuta na tafi da gidanka, a cewar ofishin ‘yan sanda dake West Hills.

Jami’in tsaro mai suna Christopher Kesslak ya bayyana cewa karar da aka shigar ga mai laifi McIntosh shine na watsa wa yaron man fetur da fadar maganganu masu nasaba da cinna masa wuta.

Wani mutum da ya isa gidan kafin ‘yan sanda su isa, ya bayyana cewa McIntosh ya ce “ida baza mu iya fitar da aljanin ba, to zan cinna wa yaron wuta har sai aljanin ya fita”.

Mutumin ya ce yayi kokarin dakatar da McIntosh, amma wanda ake tuhuma din ya kai mishi naushi kuma ya buga shi a kansa da bulo, kafin ya tsare. Jami’an tsaro sun bayyana cewa an samu ciwo bangaren hagu na gefen kan mutumin, da kuma hannun sa da kusa da kunnen sa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *