Mutumin da yafi kowa gajerta a duniya ya kara komawa matsayinsa a mujallar Guinness makon da ya wuce biyo bayan rasuwar wanda yake da kujera a baya.

Dan kasar Colombia Edward Nino Harnandez mai shekaru 34 ya karfi takardar shaida haka a hukumance Laraba a babban birnin Bogota a lokacin da yake tare da iyalansa da likitansa. Yana da tsawo kafa 2 da inci 4, alamun dake nina ya dan kara tsawo.

A shekarar 2010 lokacin da ya fara hawa wannan kujera, an gwada shi da tsawon kafa 2 da inci 3 kamar yadda mujallar ta rawaito.

Khagandra Thapa Magar na kasar Nepal ne wanda ya rike wannan matsayi a baya-bayannan inda yake da tsawo kafa 2 da inci 2. Ya rasu a watan Janairu, lamarin da ya sa Harnandez ya koma matsayinsa na mutumin da yafi kowa gajerta a duniya.

Hernandez dai yana da cutar “hypothyroidism” inda jikinsa ya gagara samar da isassun sinadaran dake taimakawa tsawo tun yana da shekaru 4.

Yace “ina amfani da murmushi na wajen takalar rayuwa. Ina yi wa kowa murmushi sosai, shine abunda jama’a suke sha’awa a tare da ni. Zan iya cimma duk wani abu da na saka a gaba. Komai zai iya yiwuwa, kuma girman jiki ba wani abu bane. Ina so mutanen da na hadu da su su san asalin ko ni wane ne. Mai karamin jiki da katuwar zuciya.”

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *