Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya bayyana cewa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatinsa da ‘yan bindigar da suka addabi jihar ta ruguje Larabannan.

Ran 28 ga watan Agustan 2019 ne Masarin ya gana da wakilan ‘yan bindigar dake addabar kananan hukumomin jihar guda takwas.

Ya bayyana aniyar ziyarar itace kiran hankulan ‘yan bindigar akan su cigaba da girmama afuwar da gwamnatinsa ta yi musu.

Amma a ganawa da kafofin yada labarai Laraban nan, Masari ya bayyana cewa gwamnatin shi ta dena ganawa akan wata duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattaba wa hannu akai, tunda ‘yan bindigan basu rike alkawari ba.

Gwamnan yace yarjejeniyar da aka amince akai tsakanin gwamnatin Jihar da ‘yan bindigar ta amince akan cewa ‘yan bindigan zasu tuba kuma zasu bar yankin arewa maso yammacin kasar.

Masari ya kara da cewa ‘yan bindigar sun yaudari jihar tunda basu girmama wannan yarjejeniya ba.

Ya zuwa yanzu, ‘yan bindiga na cigaba da kai hare-hare a kauyuka da garuruwa inda suka hallaka mutane da yawa, yayin da wasu suka rasa hanyoyin samun abincin su.

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Aslm
    Kamar Akwai Kus-Kure wajan mayar wa da jihohi kudin Gina tituna
    Kun rubuta dala($) kun kuma ce nera🤔
    So wanne zamu dauka?