Mai taimakawa Shugaban kasa ta fanni kafafen yada labarai Garba Shehu ne ya bayyana cewa gobarar ta tashi Alhamis dinnan ne a cikin fadar.

Bayanan sa sun kara da cewa wutar ba wata babba bace, kuma ta faru ne ta sanadiyar hadewar wayoyin wutar lantarki.

Garban ya kara da cewa hatsarin ya faru ne a wani dakin ajiya kusa da bangaren dakin ibada a cikin villa, kuma an dauki mataki na gaggawa wajen magance ta.

An yi amfani da hodar kashe wuta kafin motocin kwana-kwana dake girke a cikin fadar su iso.

Sannan ya kara da cewa ba’a samu rauni ko wata mummunar asara ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *