An bukaci duka wuraren addini akan su bi sharruda 29 na baiwa juna tazara domin kare al-umma daga yaduwar COVID-19 kafin masallatai da majami’ai su bude a Abuja, a cewar Babban Birnin Tarayyar.

Hukumomin Abuja sun gana da shuwagabannin addini Musulmai da Kirista Alhamis dinnan domin amincewa akan matakan da za’a bi kafin a bude wuraren addini.

Sharrudan sune:

 1. Dole sai an tabbatar da kasancewar ruwan famfo da sabulu ko ruwan sabulu a wuraren shiga da fita na duk wani waje inda ake haduwa da yawa a ciki harda bahaya.
 2. Dole jama’a su killace hannu kafin su shiga.
 3. Dole sai anyi amfani da takunkumin rufe hanci da baki.
 4. Ba’a bada shawarar taba juna ba, kamar gaisawa da hannu, runguma, sumbace, bada abubuwa, amfani da abu daya kamar dadduma, kayan kida da makurfo.
 5. Dole sai an tsagaita adadin mutane da zasu kasance a wuraren addini domin tabbatar da tazarar mita biyu tsakanin mutum daya da mutum daya.
 6. Dole shugabanni su shata wuraren da jama’a zasu kasance koda a gida daya suke, domin warewa daga juna.
 7. Dole sai an tantance adadin masu taimakawa wajen tabbatar da sharrudan domin amfani da dai-dai adadin da ake bukata, kuma a tabbatar babu wanda yake da wata rashin lafiya, sannan babu wanda ya fi shekaru 55.
 8. A tsagaita adadin lokacin kasancewa a wajen addini, sannan a tabbatar sau daya aka gudanar bauta a waje daya.
 9. Majami’ai zasu bude daga karfe 5 na safe su rufe 8 na dare, kuma kar kowace bauta ta wuce sama da sa’a daya, da tazarar minti talatin domin tsaftace wajen.
 10. Masallatai zasu bude mintuna 15 kafin Sallar farilla, kuma su rufe mintuna 10 bayan idarwa.
 11. Lokacin jira tsakanin Salloli kar ya wuce minti 10, kuma a rage tsawon lokacin Sallah domin rage haduwar jama’a.
 12. Dangane da Sallar Juma’a, masallatai zasu bude minti 20 kafin Sallah, su kuma rufe minti 20 bayan an idar, sannan kar huduba ya wuce sa’a 1.
 13. Makarantun addini zasu kasance a rufe.
 14. Sallolin farilla ne kawai aka yarda a gudanar a masallatai.
 15. Ba a yarda da taron ibada mai yawa ba, wanda baza a iya tabbatar da bada tazara tsakanin jama’a ba.
 16. Idan za’a motsa a wuraren addini, a yi a hankali kuma a bada tazara yadda jama’a baza su hadu ba.
 17. An bukaci masu zuwa ibada akan su yi rijistar lokacin da yafi musu dacewa su je wajen addini, sannan a gabatar da ibada akan yanar gizo domin wadanda suke son gudanarwa a gida.
 18. An bukaci majami’ai akan su samar da kofar shiga wajen ibada daban, da ta fita daban, kuma a jagoranci shige da ficen mutane yadda baza a kusanci juna ba.
 19. An haramta taro kafin ibada da bayan an kammala.
 20. Shaguna da sana’o’in da suke wuraren ibada zasu kasance a rufe.
 21. Dangane da mutanen da basu da karfi ko lafiya sosai, kamar masu shekaru 55 zuwa sama, ko matsala a garkuwar jikin su, ko wata rashin lafiya kamar ciwon suga ko ciwon zuwa, an bukaci su zauna a gida ko su gudanar da ibadar ta yanar gizo, ko kuma a cikin mota daura da wajen ibada.
 22. A tabbatar babu tabarma ko kafet a kasa domin saukin tsaftace wurin da ma kujeru da tebura.
 23. A bar taga a bude domin iska ta ringa shiga tana fita.
 24. A yawaita tsaftace wuraren da jama’a suke tabawa musamman a bahaya.
 25. Ana bukatar masu share share da goge goge suyi amfani da sinadarin bilic mai karfin kaso 1000 a cikin 1,000,000 domin tsaftace datti. A kuma hana duk wani daga cikin su yin aikin idan ya kamu da cutar domin kiyaye yaduwarta.
 26. Ana baiwa masu zuwa wuraren ibada shawara akan kar su je idan suna da alamomin cutar COVID-19.
 27. Ba za a bar duk wani wanda zafin jikin shi ya wuce yadda ya kamata ba, ko aka ga yana da alamun cuta shiga wajen ibada.
 28. Za’a dauki bayanan duk wanda yaje wajen ibada domin bin sawun wadanda yake tare da su da wadanda ya gana da su idan aka same shi da cutar koda daga baya ne.
 29. Ana bada shawarar kiyaye ziyarce-ziyarcen addini daga malamai zuwa gidajen jama’a.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *