Alhamis dinnan ne Shugaban rundunar sojojin sama na Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar ya bai wa dakarun sama da kasa umarnin zaluko da hallaka duk wadanda ake zaton ‘yan bindiga ne, kuma a ba shi rahoto kowani mako akan ayyukan da suke yi.

Da yake magana ne a ziyarar da ya kai sansanin sojojin sama da ke gudanar da aikin Hadarin Daji na rundunar sojojin sama ta 213 dake Katsina, Abubakar yace “dole sai mun nemo duk inda ‘yan bindiga suke, kuma mun kashe su kamar yadda ya kamata”.

“Kar muyi kasa a gwiwa har sai jama’a sun samu damar tafiyar da sana’o’in su ba tare da fargabar hari ba daga ‘yan bindiga ko masu garkuwa da mutane” a cewar shi.

Yace za’ a samar da duka kayan zirga-zirga da makamai domin gudanar da aikin, inda ya kara da cewa “bai kamata a baiwa ‘yan bindiga da masu karya doka damar cigaba da kar hare-hare”.

A lokacin da yake rokon mutanen gari akan samar da sahihan bayanai akan ‘yan bindigar, Abubakar yace “’yan bindiga ba fatalwa bane, masu garkuwa da mutane ba fatalwa bane; Idan muka samu sahihan bayanai akan su, wannan zai taimaka mana matuka yadda duka mutanen kasar nan zasu zauna lafiya”.

Gwamnatin jihar ta janye daga yarjejeniyar zaman lafiya da ta rattaba wa hannu da ‘yan bindigar biyo bayan sababbin hare-hare masu yawa da suka hallaka mutane.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *