Biyo bayan amincewa jihohi biyar domin basu dala biliyan dari da arba’in da takwas na gina manyan tituna da suka hada jihohi a kasar baki, to gwamnatin Buhari tayi amai ta lashe.

Ministan al-adu da sadarwa ne, Lai Mohammed wanda ya tattauna da manema labarai akan tattaunawar yanar gizo da shugaba Buhari yayi, inda yace duk wata jiha da take so ta gina tituna dake jihohi ba tare da niyyar mayar da kudin zuwa ga gwamnatin tarayya ba, to dole sai ta samu izinin gwamnatin tarayyan sabuda alhakin lura da aikin ya fada kan Ma’aikatar Ayyuka da Muhalli.

Lai ya kuma bayyana cewa kwamitin zartaswa ta kasa ta amince da biyan jihohi biyar nera biliyan dari da arba’in da takwas da suka kashe akan tituna sakamakon wadannan sababbin sharrudan.

Wannan ya sa za’a baiwa Kuros Ribas biliyan goma sha takwas da miliyan dari uku, Ondo kuma zata samu biliyan bakwai da miliyan dari takwas, sannan Bayalsa zata karbi biliyan talatin da takwas da jihar Ribas mai karbar biliyan saba’in da takwas da miliyan dari tara.

Ministan ya kara da cewa tuni aka biya jihohi talatin daya sama da nera biliyan dari biyar zuwa ga jihohi talatin da daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *