Majalisar dokokin jihar Zamfara ta sauke shugabannin kananan hukumomi 14 dake fadin jihar.

Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Hudu Yahaya, ya tabbatar da haka.

Wannan ya biyo bayan rahoton na musamman da ya zargi shugabannin kananan hukumomin da gudanar da kudade ba bisa ka’ida ba.

Har ila yau wani rahoton tsaro ya zargi shugabannin kananan hukumomin da rashin maida hankali a yaki da ‘yan ta’adda da ake a kananan hukumomin.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnan jihar ya nada sabbin shigabannin rikon kwarya, tare da sanya ranar gudanar da zabe a kananan hukumomin jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *