Tsohon gwamna Orji Uzor Kalu wanda aka samu da laifuka talatin da dara akan satar kudaden gwamnati har na nera biliyan bakwai da miliyan dari shida tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 ya fito daga kurkuku.

Hukumar Kurkukun ce ta tabbatar da hakan ta bakin kakakin ta Augustine Chukwudi Njoku a yammacin Laraba.

Ya bayyana cewa an sako Uzor Kalun ne sakamakon umarni da kotu ta bayar.

A baya bayannan, daya daga cikin lauyoyin Kalu wanda ya nemi a boye sunan sa, ya bayyana cewa Uzor wanda Sanata ne dake wakiltar Abiya ta arewa a karkashin jam’iyyar APC, an sako shi ba tare da bata lokaci ba bayan kotun ta bada umarnin sakin sa.

Wata kotun kasa jihar Legas a Talatannan ne ta bada umarnin sakin Kalu nan take, biyo bayan takardar da shugaban gungun lauyoyin sa Lateef Fagbemi SAN ya shigar na neman sako shi.

Hukumar EFCC bata kalubalanci sakin ba.

Hakan ya sa Alkali Mohammad Liman ya amince da sakin sa kamar yadda aka nema.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *