Tambarin Shelkwatar Hukumar Tsaron Najeriya
Hoto: Shafin tiwitar @DefenceInfoNG

Rundunar Sojin Najeriya ta kashe kwamandojin kungiya Boko Haram a Borno.

Shelkwatar rundunar ta ce dakarunta na rundunar Operation Lafiya Dole da ke arewa maso gabashin Najeriya ne suka yi nasarar kashe kwamandojin ƙungiyar guda uku.

A sanarwar da rundunar ta fitar, ta ce lamarin ya faru ne bayan Boko Haram ta kai hari a yankin Banki Junction, inda sojoji suka mayar musu da martani kuma suka yi nasarar kashe kwamandojin Boko Haram na ɓangaren Abubakar Shekau.

A cewar shelkwatar tsaron Manzar Halid da Amir Abu Fatima da Nicap na daga cikin manyan mayaƙan ƙungiyar da aka kashe.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *