Hukumar raya yankin Neja Delta ta bayyana cewa tsohon darektan ta a harkokin kudi da gudanarwa Ibanga Bassey Etang, ya rasu ne sakamakon annobar cutar COVID-19.

Rahotannin baya sun nuna cewa Etang ya rasu ne Alhamis dinnan daga cutar da ba’a bayyana ba, amma ana kyautata zaton COVID-19 ce a asibitin koyarwa na Jami’ar Ribas dake Fatakwal.

A sanarwa da hukumar tayi ta bakin jami’in ta Charles Odili, an samu bayanin cewa gwaji da aka gudanar ya nuna cewa Etang na dauke da cutar Korona.

Bayanai sun nuna cewa jim kadan bayan rasuwar Etang, an rufe shedkwatar ma’aikatar hukumar inda aka umarci duka ma’aikata su tafi gida domin kebewa.

Shaidu daga cikin ma’aikatar sun kwarmato cewa Etang ya samu kanshi a cikin halin rashin lafiya ne misalign karfe biyu na daren alhamis, inda aka garzaya da shi zuwa asibitin jiha, sannan ba’a yi sa’o’i uku ba yace ga garin ku.

A halin yanzu dai hukumar ta NDDC na samun matsin lamba saboda kazafin cin hanci da rashawa da ake mata na shekaru, ganin cewa babu wani aikin a zo a gani da aka ce tayi biyo bayan makudan kudade da aka bata, kuma yanzu haka tana shan bincike da majalisar tarayya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *