Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa ya bayyana cewa kisar Hakimin Yantumaki Abubakar Atiku ba zai kashe wa gwamnatin gwiwa ba a yakin da take yi yanzu haka da ‘yan bindiga da suka addabi jihar.

A sanarwa da ya fitar ta hannun darektan sa na yada labarai, ya ce masu kashe mutane da karya doka zasu fuskanci hukunci.

Yayi kira ga jama’a akan su bada hadin kai ga gwamanti da jami’an tsaro domin yaki da ta’addanci ta bada bayanai masu amfani da zasu taimaka wajen shawo kan wannan tashin hankalin.

Da yake bayyana alhinin sa na rashin hakimin, ya kwatanta shi a matsalin mai son zaman lafiya, mara son kai kuma mai aiki tukuru wanda ya taimaka sosai wajen tabbatar da zaman lafiya a yankinsa.

A wani yanayi mai kamar wannan, yayi ta’aziya ga iyalan tsohon shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Batsari Alhaji Abdulhamid Ruma wanda ‘yan bindiga suka kai masa hari kuma suka kashe shi a kusa da Batsari Asabar dinnan, inda ya bayyana cewa an mayar da martani cikin gaggawa tare da taimakon tsofaffin ‘yan bindigan wadanda suka tuba, kuma suke taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da wannan lamari a jihar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *