Maza dake tara gashi a fuska na dalilin samun karfin gwiwa ba don mata sun fi son mazan dake da dashi ba.

Wani nazari ya nuna cewa ta yiwu gashi a fuska yana fito wa maza ne domin taimaka wa mazan dake jin yunwa jurar naushi, kamar yadda binciken ya nuna a wata takarda da aka buga a mujallar “Integrative Organismal Biology”. Sakamakon binciken yazo ne daga gwaje-gwaje da dama da masu binciken suka yi akan juriyar bil adama, a ciki harda da juriyar karbar naushi a fuska da kuma amfani da hannu a matsayin makami.

“Mun gano cewa abu mai gashi yafi jurar duka idan aka kwatanta da wanda bashi da shi” a cewar Ethan Beseris da Steven Naleway da David Carrier, kwararru a binciken kimiyya.

Amma abun murna shine babu bil-adaman da aka kaiwa naushi a lokacin wannan bincike, sai dai anyi amfani da kwarangwal din da aka kera sannan aka lullube shi da gashin tumaki. Domin kwatanta naushi, sai aka ringa jefa wani abu mai nauyi akan kumatu sannan aka auna karfin naushin da na’u’ra.

An gano cewa fuska mara gashi na jurar naushi da kaso goma sha shida cikin dari, kuma mai gashi yafi jure karfin naushi da kaso talatin da bakwai cikin dari.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *