Yayin da miliyoyin mutane suke aiki da gida saboda rufe ma’aikatu da aka yi saboda dakile yaduwar cutar Korona, daya daga cikin abubuwan da mutane da yawa basu yi tunani ba shine na irin kayan abinci da suka bari a wajen aiki da ka iya rubewa.

Zama a gida ya ba wa mutane kwanciyar hankali tunda baza su damu ba ko sun bar kofar gida a bude, ko kuma murhu a kunne, amma wata mata a burtaniya ta nuna damuwar ta akan ayabar da ta share makonni tara a ofishin ta, biyo bayan mancewa da tayi wajen daukowa da kai gida.

Mhairi-Louise Brennan ‘yar Glasgow dake Sukotlan da damu matuka, inda har ta buga a shafin tiwita, lamarin da ya sama mata magoya baya har suna ta tsokanar ta da kuma tunanin yadda siffar ayabar zata kasance bayan ta koma ofishin.

Bayan ta samu dama, Brennan ta koma ofishin inda ta dauko hoton rubabbar ayabar da yanzu ta yi baki kirin, don ma dadinta kayan ciki basu fito ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *