ZA A BUDE BANKUNA DA ZIRGA-ZIRGAR JIRAGE A CIKIN NAJERIYA

Gwamnatin Tarayya ta amince da bude tashoshin jiragen sama na cikin gida domin fara zirga-zirga ranar 21 ga wannan wata.

Shugaban kwamitin PTF da shugaban kasa ya nada Dr. Sani Aliyu ya bayyana hakan ne a Abuja Litinin dinnan a tattaunawa da kwamitin yayi.

Amma ya kara da cewa har yanzu ba a amince da zirga-zirga tsakanin jihohi ba.

Haka zalika ya kara da cewa za a ci gaba da zaman gida a duk fadin kasar daga karfe takwas na safe, zuwa shida na yamma, lamarin da ya nuna cigaba idan aka kwatanta da baya wato daga karfe goma na safe zuwa karfe hudu na yamma.

Ya jaddada cewa duk wani mai aiki mai muhimmanci zai iya fita a daidai wannan lokacin da kasar ke shiga sashe na biyu na sassauta zaman gidan dole.

Kamar yadda ya bayyana, duk masu aiki a bangaren kiwon lafiya da kafafen yada labarai da bangarorin kasa masu muhimmanci suna cikin masu aiki mai matukar muhimmanci. Har yanzu ba’a yarda sama da mutane ashirin su hadu a wajen ibada ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *