Hukumar ‘yan Sanda ta jihar Adamawa ta bayyana cewa ta kama mutanen da ake zarginsu da garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Da take bayyana su a bainin jama’a Litinin dinnan, kwamishinan ‘yan sandar Jihar Olugbenga Adeyanju yace rundunar shi tayi amfani da sahihan bayanai ne domin tsarewa da kamawa masu laifi ta yin amfani da ‘yan bijilante da mafarauta.

Kamar yadda yace, ‘yan sandan sun kuma fatattaki wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen da wuraren da suke boyewa a tsaunuka inda suka samo makamai masu hadari.

“Mun kai musu farmaki a Dutsin Yadim, wajen da yayi kaurin suna dangane da masu garkuwa da mutane, a nan muka kama mutum bakwai sannan muka samu bindigogi kirar AK47 guda uku.

“Mun kuma samo bindiga samfurin Dane, da wani dan karamin bindiga da aka kera da hannu, da babura guda biyu.

“Rundunar mu ta kuma tsare mutumin da yayi garkuwa da Sule Haro, Pastor Ishaya da wata wata Solomi Ishaya, kafin ya kashe mijinta a Mararraban Bokki dake karamar hukumar Gombi a watan Afrilun 2020.

“Wadannan mutanen sune suka sace Aminu Hassan, Isah Usman da Hamza Adamu, dak mazauna Uba dake karamar hukumar Hong inda suka nemi a basu nera miliyan goma.

Wadannan mutane sun kuma bayyana cewa sune suka yi garkuwa da Dodde Zumo, da Ya’u Mohammadu, duk mazauna Zumo dake karamar hukumar Maiha, kuma har aka basu kudin fansa na nera miliyan daya a watan Maris din 2020 kafin a kama su.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *