Yanzu haka ta yiwu ya barar da siyasar shi.

Maiguwan wani gari dake kasar Peru, ya kwanta a cikin akwatin gawa sanye da takunkumin rufe hanci da baki kamar wani gawar Korona, domin gujewa kama shi saboda ya keta dokar zauna-a-gida, wadda ya kamata a ce da shi ake kokarin tabbatar da ita.

Jaime Rolando Urbina Torres ya fita sharholiya ne da abokan shi a garin Tantara daren Litinin inda yayi kamar ya mutu domin kar ‘yan sanda su kama shi a lokacin da aka kai musu sumame saboda saba dokokin kiwon lafiya da aka gindaya, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Mai unguwan, wanda dama yana tsakiyar shan suka saboda an neme shi an rasa a wannan lokaci na annoba, to yanzu dai akwai hoton shi da aka dauka yana kwance a cikin akwatin gawa idanun shi rufe. An tsare Torres ana tuhumar shi da laifin karya dokar zauna a gida.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *