A ranar 25 ga watan Mayun 2020 ne wani farar fatar Dan Sanda Derek Chauvin ya hallaka bakar fata George Floyd a Amurka.

A ranar 25 ga watan Mayu da ya gabata ne na shekarar nan ta 2020, wani farar fatar Dan Sanda mai suna Derek Chauvin ya hallaka wani bakar fata mai suna George Floyd har lahira bayan ya sa gwiwa ya murkushe sangalalin wuyansa bakar fatar a kwance a kasa cikin dabaibayin ankwar ‘yan sanda da ke makale a hannayensa.

Marigayi George Floyd
Hoto: Shafin yanar gizon jaridar New York Times

Inda wannan bawan Allah yayi ta kakari a kasa yana ta maimaita cewa, “Bana iya numfashi.” Nan dai George ya gama ‘yan shure-shurensa na neman dauki, amma hakan bata samu ba har dai rai yayi halinsa bayan gwiwar Derek ta share tsawo mintuna 8 da dakika 46.

Dan Sanda Derek Chauvin danne da wuyan George Floyd a jihar Minnesota.
Hoto: Shafukin yanar gizo

Wannan lamari ya faru ne a unguwar Powderhorn ta karamar hukumar Hennepin da ke Kudu da cikin kwaryar birnin Minneapolis na jihar Minnesota a kasar Amurka, a lokacin da shi Baturen dan sandan yayi kokarin kamawa tare da tafiya da shi bakar fatar Mista George tare da taimakon wasu ‘yan sandan Tou Thao, Alexandra Kueng da kuma Thomas K. Lane da ke aiki tare da jami’i Chauvin.

Bisa koken masu shigar da karar aikata kasassaba lokacin shigar da kararsu, sun bayyana cewa, daga cikin wadannan mintuna da Floyd ke kwance a kasa fuskarsa na dankwafe a kasa ga kokon gwiwar dan sandan a kan dokin wuyan bakar fatar, mintuna 2 da dakiku 53 tuni sun faru ne bayan ma wannan mutum ya mace.

Masu zanga-zanga a lokacin da suka yi rubuce-rubucen bacin rai a kan kwalta hanyar zuwa fadar shugaban Amurka.
Hoto: Usman Kabara

Bayan bakar fatar ya ce ga garinku nan ne fa, wannan abu ya watsu kamar wutar daji ta hanyar watsuwar wasu hotunan bidiyo da makamantansu a shafukan yanar gizo wadanda ‘yan gaza gani suka dauka da wayoyinsu na tafi da gidanka. Inda a karshe dai mutane suka botsare da fara zanga-zangar nuna rashin amincewa da wannan abu da ya faru.

Bisa wasu majiyoyin na ‘yan sanda, sun nuna cewa sun je kama Floyd ne a wajen sayar da abinci, bisa zargin cewa wani ma’aikacin shago ya kira wayar jami’an tsaron ne a kan wai bakar fatar yana son amfani ko kashe jabun takardar kudin Amurka ta Dalar 20.

To a cewar majiyar ‘yan sandan sun yi kokarin kama shi mutumin lami-lafiya amma ya tubure tare da kin yarda ya fito daga motarsa balle ma ya shiga motarsu. Wannan ne ya ja suka yi amfani da karfin tuwo wajen kai mutumin kasa tare da buga masa ankwa hade da murkushe shi.

A lokacin da masu zanga-zangar ke rabawa juna ruwan sha don jika makoshi.
Hoto: Usman Kabara

Sai daiu binciken wasu kafofin yada labaran sun ruwaito cewa, akwai kyamarorin da ke makale suna kallon kurilla gaban shaguna daga wani gefe, ba a ga inda shi wannan bakar fatar Ba’amurken ya yi wata gardama ba in ji wasu majiyoyin ‘yan gaza ganin.

Wannan zanga-zangar da ta faro daga garin na Mineapolis ta watsu a wasu sassan jihohin Amurka wanda mahalartanta suka hada da farare da bakaken fata Amurkawa. Ranar 29 ga Mayu ne, wato kwanaki hudu bayan mutuwar Geoge a ka kama shi Derek da ya aikata kisan kan tare da sallamarsa da da sauran ‘yan sandan nan guda uku daga aiki.

Bugu da kari an shigar da kararsa bisa zargin kisan kai a mataki na uku wanda suke fassarawa da kisan ba da gangan ba amma na rashin la’akari da girmama rayuwar bil’adama da ka iya fadawa hatsari. Sai kuma wani zargin kisan a mataki na biyu da ake kira da kisan ganganci wanda ba da niyya ba.

Lokacin da jami’an tsaro suka yi wa fadar shugaban Amurka kawanyar kariya.
Hoto: Usman Kabara

Tuni dai jami’an hukumar binciken manyan laifuffuka a Amurka ta FBI suka dukufa binciken gaskiyar abin da ya faru na wannan yamutsin da ya harzuka masu fafutukar ganin an sami daidaito tsakanin rayuwar fari da baki da ma duk wani jinsi ko launin fata. Sannan ana sa ran su kansu ‘yan sandan da suka taya Chauvin murkushe Floyd za su fuskanci tuhuma game da faruwar lamarin.

Lokacin da zanga-zangar kisan da a ka yiwa George ta faro a ranar 26 ga watan na Mayun 2020, ta fara ne a matsayin ta lumana, amma kafin kowa ya farga zuwa yammacin ranar ta rikide zuwa ta fashe-fashe da kone-kone tare da yi wa ‘yan sanda ruwan duwatsu. Su kuma ‘yan sanda suka ci gaba da harba barkonon tsohuwa da harsasan roba don tarwatsa masu boren.

Zanga-zangar ta sami karbuwa a wasu garuruwa masu yawa a Amurka don nuna Allah wadai da karfa-karfar da ‘yan sanda ke yi wajen gallazawa jama’a musamman bakaken fata, wanda jama’a ke kallo a matsayin wani salon nuna kyama da wariyar launin fata cikin hikimar da ba kowa zai gane ana fake wa da guzuma ba ne ana harbin karsana.

Masu zanga-zanga a lokacin da suka yi rubuce-rubucen bacin rai a jikin bango a kusa da fadar shugaban Amurka.
Hoto: Usman Kabara

Ba dai wannan ne karon farko da a ka taba samun jami’in dan sanda ya murkushe bakar fata da sunan kame ba har sai ya garzaya barzahu. Domin idan an tuna ko a shekarar 2014 sai da wani mai suna Eric Garner ya bakunci lahira a birnin New York, sakamakon irin wannan karfa-karfar ta wasu ‘yan sanda a Amurka.

A halin da a ke ciki dai wannan zanga-zangar bacin ran ta ja an saka dokar hana fita da zarar dare yayi har zuwa safiya, ciki har da Washington DC wanda shine babban birnin na Amurka. Ana sa ran gwamnati ta dau wannan mataki ne saboda gudun kar boren ya fi karfin dakatarwa.

Wasu masu fashin bakin al’amuran yau da kullum a Amurka na zargin shugaba Donald Trump da yin ingiza mai kantu ruwa wajen yi kausasan maganganun da ke farfado da tsana da tsangwa tare da wariyar launin fata a kasar da kowa ke ikirarin ‘yanci da walwala sannan duniya ta ke kallo a matsayin jagora kan maganar ‘yancin bai daya ga kowa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *