Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ta leka gidaje dubu ashirin da tara da dari bakwai da saba’in da daya a kananan hukumomi tare inda aka tabbatar da samun cutar Korona, domin zurfafa bincike don neman wadanda ka kamu da ita.

Manema labarai sun bayyana cewa wadannan kananan hukumomi tara sun kunshi Igabi, Chikun, Kaduna ta arewa, Kaduna ta kudu, Makarfi, Giwa, Sabon-Gari, Soba da Zariya.

Ma’aikatar lafiya ta jihar ta bayyana cewa jami’an kiwon lafiya sun binciki wadannan garuruwa ne domin gwaji da neman masu alamun cutar Korona, inda suka kara cewa sunyi wa mutane dari biyu da tasa’in da bakwai masu zazzafi ko ciwon makwogoro gwajin Korona.

Kwamishinan lafiya ta jihar Dr. Amina Mohammed Bolani ta bayyana cewa za’a iya samun karin adadin mutane dake dauke da Korona, saboda har yanzu ana cigaba da gwada jama’a.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *