Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ganawa da Shugabanni da manyan ‘yan Kasuwa na Jihar Kano kan yadda za a bi don dakile yaduwar cutar coronavirus a ya yin bude Kasuwanni dake fadin jihar.

Cikin Jawabansu yan Kasuwar sun shirya raba takunkumin rufe baki da hanci ga masu shiga kasuwannin a wadannan ranakun da kuma ci gaba da ba Gwamnati goyon baya don kaucewa Yaduwar cutar a Jihar.

Gwamna ya jajantawa ‘yan Kasuwan bisa yadda mafi yawa suka yi asara tare da addu’ar Allah ya kawo karshen wannan annobar.

Ya ce amfani da kyakkyawan tsari a kasuwar shine zai ba gwamnati damar sake sassauta dokar.

Daga bisani ya umarci Kwamishinan muhalli daya hadakai da Shugabannin Kasuwannin domin ganin Gwamnatin ta karawa kasuwannin kayayyakin kariya daga kamuwa da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *