Hamshakin attajirin nan Bill Gates na ci gaba da taimaka wa yara a nahiyar Afirka da magunguna da tallafawa masu kananan sana’o’i da ma baiwa mata marasa karfi jari domin fitowa daga kangin talauci.

Hamshakin attajirin nan Bill Gates na ci gaba da taimaka wa yara a nahiyar Afirka da magunguna da tallafawa masu kananan sana’o’i da ma baiwa mata marasa karfi jari domin fitowa daga kangin talauci.

Cututtuka kamar zazzabin cizon sauro da kanjamau da polio da masu wasu cututtukan masu yaduwa sun ragu sakamakon ayyukan da Gates din yayi. Mutumin ya kasance mai basira da kuma taimakon al-umma. Duk lokacin da aka samu wani bala’i ko annoba, yana bada nashi irin gudunmuwar wajen taimakawa.

Duk da haka, Gates na samun kazafi daga wasu tsirarun mutane suna masu cewa yana yunkurin tarwatsa al-ummar duniya ne da COVID-19. Sun kuma kara da cewa Gates yana so ya saka wata ‘yar na’ura a cikin jikin bil adama domin ya samu ikon duk bil adama. Sai dai wadannan jita jita basu da alamar gaskiya, amma kuma jama’a da yawa sun yadda da hakan.

Ko me yasa dan adam zai kashe wani domin ya samu iko akan shi? Gaskiyar magana shine mutane masu kirkire kirkiren fasaha kamar Gates din suna da iko a rayukan mu a yanzu haka. Baza ka iya samun ilimin zamani ba a wannan lokaci ba tare da amfani da na’u’rorin da kamfanin Bill Gates din ya hada.

Sai dai wadannan kazafce-kazafcen basu da tushe saboda dalilai da dama. Duba da irin gudunmuwar da baiwa masu bukata, musamman mata da marasa karfi da yara, da taimakawa wajen bunkasa ilimi da rage radadin talauci, musamman a nahiyar Afrika, hakan ya sha banban da abubuwan da ake zargin shi da su.

Kungiyar agaji ta Bill Gates na kashe sama da dala biliyan biyu kowace shekara wajen taimakawa jama’a a nahiyar Afirka. Haka zalika ya saka hannu a takardar dake cewa idan yam utu, to kaso tasa’in cikin dari na arzikin shi za’a yi amfani da sune wajen taimako da agaji.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *