Biyo bayan daukar lauya da rubuta takardar shigar da kara na neman a biya shi Nera miliyan tara da ‘yan kai da ya kashe a lokacin da yake neman aurenta, an baiwa Zubairu Dalhatu Malamai tsohon saurayin Zainab Abdullahi Yahaya Nera miliyan goma cif domin kawo karshen wannan dambarwa.

Daya daga cikin na kusa da Hameed Ali ne Mai suna Mohammad Ajia Ibrahim, biloniya kuma shine Chairman na MAI Foundation wanda yace bazai bari a ja sunan mai gidan shi a kasa ba, saboda haka sai ya mika mishi kudin Talatannan adadin da yafi abunda Zubairu ya bukata, kuma ya tabbatar Zubairun ya saka hannu akan takardar dake tabbatar da cewa ya karba.

Idan ba’a manta ba, Zubairu ya nemi a biya shi kashe mata a shekaru ukun da suke tare, inda ya kara da cewa tana ta alkawarin aurensa ne shi yasa yake ta kashe mata arzikinsa, amma a cikin zuciyarta, ta san ba haka bane. Ya kara da cewa, tunda yanzu ta yanke shawarar auren wani mutum daban ba shi ba, to yana mata murna a sabon gidan ta, amma bai ji dadin fadan babu gaira babu dalili ba da ta ballo kwanaki kadan kafin auren ta, inda yace ta kira shi da sunaye, kuma ta ce masa yayi lissafin duka kudaden da ya kashe mata a matsayin bashi, yadda zata biya shi domin ya fita daga rayuwar ta.

Hakan ya sa Zubairu yayi lissafin kudaden da ya kashe mata, kuma yana bukata a biya shi. Akwai nera miliyan biyu da dubu dari bakwai da saba’in da takwas da sule hamsin na kudaden tikitin jirage zuwa Saudiyya, Dubai, China da Ingila.

Ya kuma nemi a biya shi nera miliyan daya da dubu dari biyar na kudaden jari da ya bata, da nera dubu dari biyu wanda ya bayar a madadin Dan Tsanyawa, da kuma wata dubu dari hudu na sana’ar sayar da tufafi, sannan akwai wata dubu dari biyu da tamanin kudin hayar shago dake Haneefa Plaza dake Court Road.

Mallam Zubairu ya kuma nemi Zainab ta dawo mishi da nera dubu dari uku da hamsin da ta karba aro domin ta baiwa mahaifin ta, da kuma wata dubu dari uku da hamsin na kudin hayar gida, akwai kuma wata dubu dari uku da ya bukaci ta dawo da shi wanda yace ta karba domin sayen mayafai, da kuma dubu dari uku da sittin da tayi amfani da shi a lokacin da tayi balaguro zuwa China, sannan akwai dubu dari biyar kudin sayo mota, da ma wata dubu dari biyu na jari da ya bata domin sana’ar cincin.

A gefe kuma, akwai wasu kudade da kaya suma Mallam Zubairu ya bukaci Zainab ta dawo da su. Sun kunshi nera miliyan daya da dubu dari bakwai da sittin da uku na kayan lefe, da abayoyi shida a cikin goma sha biyu da ta dauka wadanda aka dinka. Ya kuma bukaci ta dawo da katunan ID wanda ke dauke da sunayen Zainab Abdullahi Yahaya, Fatima Abdullahi Muhammed da Adnan Abdullahi Yahaya.

Akwai kuma kamfutocin laptop biyu na kamfani da yace an baiwa Zainab da Adnan Abdullahi Yahaya, da kayan kamfani, da takalmi, da set din akwatuna guda biyar, da akwati mai kirar Samsonite guda daya, da kuma faifan lambar mota na karamar hukumar Bichi.

A karshe an lissafa jimlar kudin a matsayin nera miliyan tara da dubu tamanin da daya da dari biyu da bakwai da sule arba’in da biyar (N9,081,207.45). Zubairu ya bukaci a dawo da wadannan kudaden nan take. Idan ba’a dawo da su ba, to zai garzaya da ita kotu.

Idan ba’a manta ba, a makon da ya gabata ne hotunan Shugaban Hukumar Kwastom Hamid Ali tare da sabuwar amaryar shi suka bazu a kafafen sadarwa, lamarin da ya jawo masu barkwancen yanar gizo suka ringa cewa budurwa tayi wuf da dattijon.

A halin yanzu dai, hotuna sun nuna sababbin hotunan Zainab da shugaban kwastam tare a tashar jirgin sama, da kuma ma a cikin irin karamin jirgin masu iko ko hannu da shuni da aka fi sani da “Frabet Jet” a kan hanyar su ta zuwa sabon gidan cin angwanci. 

Ra’ayi 1

Your email address will not be published. Required fields are marked *