Wani mutum a kasar Brazil da yaje asibiti a duba shi ta CT saboda ciwon baya ya baiwa mutane mamaki.

Ciwon bayan nashi ya samo asali ne daga kashin baya, amma likitoci sun gano cewa yana da koda guda uku.

Likitocin na asibitin Rim dake birnin Sao Paulo sun gano kodar hagu wadda lafiyar ta kalau, da kuma kodoji guda biyu dake makale da juna a kusa da kashin kugunsa, kamar yadda wata mujallar Ingila ta bayyana ran bakwai ga watan Mayu.

Irin wannan abu ba’a fiya gani ba, a cewar likitocin. Gano irin wannan lamari ma ba da niyya bane, saboda kasancewar yana da koda uku baya nuna wasu alamu.

Likitocin sun bayyana cewa irin ka iya faruwa ne a lokacin da ake dauke da kwan cikin jikin shi yake girma kafin ma a kyankyashe shi.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *