An tsare wata mata a jihar Pennsylvania dake Amurka Larabannan domin boye gawar kakarta a cikin freeza na tsawon shekaru goma sha biyar, yayin da iyalinta suka cigaba da karbar kudaden fanshon ta, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Kakar mai suna Glenora Reckord Delahay ta rasu a watan Maris na 2004 a garin Ardmore, a lokacin tana da shekaru 97.

Jikar Glenora mai shekaru 61, Cynthia Carolyn Black, ta gaya wa ‘yan sanda cewa sun boye gawar kakar tasu ne saboda iyalanta na bukatar kudaden fanshion da ake turo wa kakar.

Ta kara da cewa a shekara ta 2007, sun sauya wa freezar guri inda suka kaishi garin Dillsburg dake kilomita 100 daga garin nasu na Adrmore.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *