Wani saurayi wanda shugaban hukumar Kwastom din Najeriya ya kasa a wajen neman aure, ya fusata kuma ya fara shirin shigar da kara a gaban kuliya domin a fitar masa da hakkinsa na kudaden da yace ya kashe mata a lokacin da yake neman auren ta.

A takardun shigar da karar da Ofishin Lauyoyi na Buba Partners da ke Kano ya shirya, saurayin wanda sunansa da aka saka akan takardun Zubairu Dalhatu Malamai dan unguwar Durumin Zungura dake karamar hukumar birni da kewaye ya bukaci Zainab Abdullahi Yahaya ta biya kudaden da ya kashe mata a shekaru ukun da suke tare.

Inda ya kara da cewa tana ta alkawarin aurensa ne shi yasa yake ta kashe mata arzikinsa, amma a cikin zuciyarta, ta san ba haka bane. Ya kara da cewa, tunda yanzu ta yanke shawarar auren wani mutum daban ba shi ba, to yana mata murna a sabon gidan ta, amma bai ji dadin fadan babu gaira babu dalili ba da ta ballo kwanaki kadan kafin auren ta, inda yace ta kira shi da sunaye, kuma ta ce masa yayi lissafin duka kudaden da ya kashe mata a matsayin bashi, yadda zata biya shi domin ya fita daga rayuwar ta.

Hakan ya sa Zubairu yayi lissafin kudaden da ya kashe mata, kuma yana bukata a biya shi. Akwai nera miliyan biyu da dubu dari bakwai da saba’in da takwas da sule hamsin na kudaden tikitin jirage zuwa Saudiyya, Dubai, China da Ingila.

Ya kuma nemi a biya shi nera miliyan daya da dubu dari biyar na kudaden jari da ya bata, da nera dubu dari biyu wanda ya bayar a madadin Dan Tsanyawa, da kuma wata dubu dari hudu na sana’ar sayar da tufafi, sannan akwai wata dubu dari biyu da tamanin kudin hayar shago dake Haneefa Plaza dake Court Road.

Mallam Zubairu ya kuma nemi Zainab ta dawo mishi da nera dubu dari uku da hamsin da ta karba aro domin ta baiwa mahaifin ta, da kuma wata dubu dari uku da hamsin na kudin hayar gida, akwai kuma wata dubu dari uku da ya bukaci ta dawo da shi wanda yace ta karba domin sayen mayafai, da kuma dubu dari uku da sittin da tayi amfani da shi a lokacin da tayi balaguro zuwa China, sannan akwai dubu dari biyar kudin sayo mota, da ma wata dubu dari biyu na jari da ya bata domin sana’ar cincin.

A gefe kuma, akwai wasu kudade da kaya suma Mallam Zubairu ya bukaci Zainab ta dawo da su. Sun kunshi nera miliyan daya da dubu dari bakwai da sittin da uku na kayan lefe, da abayoyi shida a cikin goma sha biyu da ta dauka wadanda aka dinka. Ya kuma bukaci ta dawo da katunan ID wanda ke dauke da sunayen Zainab Abdullahi Yahaya, Fatima Abdullahi Muhammed da Adnan Abdullahi Yahaya.

Akwai kuma kamfutocin laptop biyu na kamfani da yace an baiwa Zainab da Adnan Abdullahi Yahaya, da kayan kamfani, da takalmi, da set din akwatuna guda biyar, da akwati mai kirar Samsonite guda daya, da kuma faifan lambar mota na karamar hukumar Bichi.

A karshe an lissafa jimlar kudin a matsayin nera miliyan tara da dubu tamanin da daya da dari biyu da bakwai da sule arba’in da biyar (N9,081,207.45). Zubairu ya bukaci a dawo da wadannan kudaden nan take. Idan ba’a dawo da su ba, to zai garzaya da ita kotu.

Idan ba’a manta ba, a makon da ya gabata ne hotunan Shugaban Hukumar Kwastom Hamid Ali tare da sabuwar amaryar shi suka bazu a kafafen sadarwa, lamarin da ya jawo masu barkwancen yanar gizo suka ringa cewa budurwa tayi wuf da dattijon.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *