Wani dan sanda ya fita daga hayyacin sa a jihar Legas inda ya bude wa abokan aikinsa wuta, lamarin da yayi sanadiyar kashe wani sajent.

Bayanai na nuna cewa hakan ya samo asali ne biyo bayan wani rashin jituwa da aka samu.

Sufeton wanda aka bayyana sunan shi a matsayin Monday Gabriel ya shiga hannun hukumomi.

Jami’in hulda da jama’a a Jihar Legas, DSP Bala Elkana ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa abun ya faru ne da safiyar Lahadi.

Ya kara da cewa Sufeton yayi kokarin arcewa bayan harbe-harben.

Elkana ya bayyana sunan dan sandan da ya rasu, wato Felix Okago, sannan yace raguwar sun tsira ba tare da rauni ba.

An samu labarin cewa sufeton ya harba harsashai sama da talatin.

Elkana ya kuma tabbatar da cewa an kai sufeton da yayi harbin asibitin ‘yan sanda domin bincikawa ko yana tabun hankali. Yace an fara bincike mai zurfi domin fahimtar abubuwan da suka faru gab da faruwar lamarin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *