Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sassauta dokar kulle ta mako huɗu da ya saka a Jihar Kano da zummar daƙile yaɗuwar cutar korona.

Shugaban kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da korona, kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana hakan a taron kwana-kwana da kwamitin ke gudanarwa a Abuja.

Mustapha, ya ce an shiga zango na biyu na sassauta dokar kulle a Najeriya, wanda zai yi mako huɗu nan gaba kafin a sake duba ta.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *