Iyalin mazauna jihar Florida dake Amurka sun yi mamakin yin maraba da kunama a cikin ayabar da suka saya a shagon kayan abinci.

Daga farko sun yi tunanin cewa kunamar a mace take, sai da ta fara yawo a tsakiyar daki sannan suka san cewa akwai matsala.

Tuni dai saurayin mai suna Matt Fry ya saka kunamar a kwalba kafin tayi wa kowa Illa. Ya kuma kara da cewa ya baiwa kunamar abinci, sannan ya saka masa suna Simon. Daga farko yayi niyyar ajje dabbar domin zama abokin zaman sa, amma da ya ga kunamar ta kai hari akan kasar gidan sa, yace to ya fasa.

Daga baya shine suka baiwa wata hukumar ceto dabbobi kunaman, inda aka gaya musu cewa wannan kunama na da hadari, sannan zata iya girma har na tsawon santimita goma sha biyar, sannan ana iya rasa rai idan har ta harbi mutum.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *