Wata tattabara da ake zargi da samun horo a kasar Pakistan domin kasancewa mai liken asiri, ta shiga hannun jami’an tsaro a bakin iyakar kasar Indiya a lokacin da aka gano wani zobe dake dauke da sakonni a kafar ta, kamar yadda wani rahoto ya nuna.

Tattabarar mai launin ja, wasu ‘yan kauye ne suka fara kama ta Lahadinnan a garin Manyari, dake kusa da bakin iyakar kasa da kasa dake raba Indiya da Kashmir wanda Pakistan ke da iko akai.

Duk da cewa ba’a san daga ina tattabarar ta zo ba, ana kyautata zaton tsuntsuwar ta taso ne daga Pakistan ta tsallaka zuwa Indiya.

Wani dan sanda ya bayya cewa tsuntsuwar na dauke da zobe mai lambobi da harrufa a jiki. Duk da cewa tsuntsaye basu da iyaka, kuma da yawa na yin hijira daga kasa zuwa kasa, ganin irin wannan zobe abun damuwa ne saboda tsuntsaye masu hijira basa daukar irin wannan abu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Sashen mu na Instagram:

Instagram has returned empty data. Please authorize your Instagram account in the plugin settings .