Gwamnatin Najeriya ta ba gwamnatocin jihohi damar bude kasuwanni dake fadin kasar nan.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar korona a lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi a Abuja.

Kwamitin wanda sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, ke jagoranta ya bayyana bada sanarwar ce yayin da wa’adin farko na mako biyu na sassauta dokar kulle ke cika.

Sai dai Babban Jami’in kwamitin Sani Aliyu, ya ce gwamnatin tarayya na kyautata zaton gwamnonin za su tsara yadda za a buɗe kasuwannin ta hanyar amfani da shawarwarin kwararru kan harkokin lafiya.

Kwamitin ya kara da cewa jirage za su ci gaba da zirga-zirga a tsakanin jihohi daga 21 ga watan Yuni, kuma haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi yana nan, haka kuma dokar hana fita a Abuja da Legas da Ogun za ta koma daga 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe, Makarantu kuma za su ci gaba da kasancewa a rufe, yayin da Otel-otel za su ci gaba da harkoki.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *