Gwamnatin Najeriya ta rage farashin litan mai zuwa N121.50.

Hukumar kayyade farashin man fetur PPPRA ta bayyana haka a wasikar da ta aikewa yan kasuwar mai.

Rage farashin man dai bai rasa nasaba da faduwar farashin danyen man a kasuwannin duniya.

Wannan shine karo na uku da ake rage farashin man fetur cikin wannan shekarar da muke ciki.

A watan Maris, gwamnatin tarayya ta sanar da ragin farashin man daga N145 zuwa N125.

Daga baya a ranar 31 ga Maris, an sanar da karin ragi daga N123.50 zuwa N125.00.

Suma ‘yan kasuwar man fetur din sun amince da bin umurnin gwamnati na rage farashin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *