Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya amince da bude duk kasuwannin jihar a ranakun da aka saba dage dokar hana zirga zirga.

Mai ba gwamnan jihar shawarar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana haka a shafinsa na facebook.

Sai dai Gwamnati ta dada jan hankalin mutane da su tabbatar sun saka takunkumin rufe baki da hanci wato face mask tare da ci gaba da tsarafe kai da sauran matakan da masana suka shawarta a rika dauka.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *