Wasu ‘yan bindiga sun harbe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina Abdulhamid Sani Ruwa.

Marigayin yana kan hanyarsa ne ta zuwa wani gari dake kusa da garin Batsari inda ‘yan ta’addan suka fito daga daji akan babura suka bude masa wuta.

A shekarar data gabata a irin wannan lokacin na farkon damina mahara suka kashe ‘dan uwan shugaban jam’iyyar.

Tuni aka kaishi babban asibiti inda likitoci suka tabbatar da rai yayi halin sa.

Karamar hukumar batsari ta dade tana fuskantar barazanar ‘yan bindiga inda ko a cikin azumin Muryar ‘Yanci ta kawo maku ruhoton yadda mutanen garin suka dinga hijira zuwa wasu kauyaku domin gujewa harin ‘yan bindiga

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *