Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya yi zaman jin bahasi da tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan sha’anin tsaro.


Zaman wanda ya gudana a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau, ya samu halartar dukkanin sarakunan jihar, shuwagabannin tsaro na jihar da jagororin ‘yan banga, ‘yan sa-kai da kuma shuwagabannin Fulani da tubabbun ‘yan bindiga.
A yayin zaman dai, an bayyana dukkanin dalillan afkuwar tashe-tashen hankullan da kuma hanyoyin da za a bi domin magance matsalar baki daya.


Wannan yunkurin dai na daga cikin yunkurin gwamnatin jihar na tabbatar da al’umma sun samu damar yin walwala kamar yadda ya dace musamman ganin yadda lokacin noma ke gabatowa.


Zaman dai ya samu gagarumar nasara, inda dukkanin bangarorin su ka yi alkawarin za su taimaka domin ganin jihar ta zauna lafiya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *