Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Jim kadan yana kammala gwamnan jihar ta Sokoto ya bayyana cewa shi ya nemi ganawa da shugaban, amma bai bayyana dalilin ganawar ba, sai dai wasu da daman a ganin ganawar ba ta rasa nasaba da yawaitar ayyukan ta’addanci a jihar.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman har da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari.

Tuni dai shugaba Buhari ya umurci rundunar sojin Najeriya da ta gaggauta kawo karshen ‘yan ta’addan da suka addabi jihar da ma sauran jihohin yankin Arewa maso yamma.  

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *