Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce taimakon kasashen da suka ci gaba ta bangaren kudi da kayayyakin aiki ga kasashen dake tasowa zai taimaka wajen yaki da annobar korona.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a Garba Shehu, ya ce shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin ganawar kasashe akalla 50 ta fasahar zamani wanda kasashen Canada, Jamaica da Sakataren majalisar dinkin duniya suka shirya.

A lokacin da yake magana, shugaba Buhari ya jaddada bukatar da take akwai ga kasashen da suka ci gaba na yafewa kasashe masu tasowa musamman kasashen Afrika basussukan da suke binsu.

Sannan ya yabawa kasashen duniya da bangarori masu zaman kansu da suka taimakawa bangaren tattalin arziki, lafiya da kuma kokarin da gwamnatin Najeriya take na yaki da cutar.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *