Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tare da hadin gwiwar jami’an soji da jami’an hukumar tsaron farin kaya DSS sun kama masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba 250.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Usman Nagoggo, ya sanar da haka a lokacin da yake gabatar da mutane ga manema labarai a shelkwatar rundunar dake Gusau.

Ya ce a ranar 21 ga wannan watan kwamandan rundunar soji ta 1 dake Gusau Janar  O. M. Bello ya jagoranci tawagar da ta kunshi jami’an soji, na ‘yan sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya kai samame wuraren hakar ma’adanai a kananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Gummi.

Ya ce samamen da aka kai Kawaye, Zugu, Dan Kamfani da Daki Takwas ya yi sanadiyyar kama mutanen.

Kwamishinan yawancin wadanda aka Kaman sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.  

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *