Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers ta kama wasu masu fashin teku 17 a wani samame da ta kai maboyarsu dake  yankin.

Mai Magana da yawun rundunar Nnamdi Omoni, ya tabbatar da kamen a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Port Harcourt babban birnin jihar.

Ya ce ‘yan ta’addan na daga cikin wadanda suka kitsa kai hare-hare kan jami’an ‘yan sanda a baya-bayan nan.

Omoni ya ce daga cikin kayayyakin da aka kwace daga hannun ‘yan ta’addan akwai bindigogi kirar AK47, da alburusai da wayoyi da kuma kudi naira dubu 50.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Joseph Mukan, ya bukaci al’ummomin jihar da su ci gaba da yin taka tsantsan da ayyukan ta’addancin masu fashin teku a yankin.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *